Uncategorized

Amarya Ta Haihu Awa 2 Kafin Daurin Aure A NajeriyaAmaryar sunan ta Misis Chinezu Adeolisa, mijin kuma sunan sa Mista Odeolisa

Lamarin ya auku ne a garin auku a garin Awo Idemili na jihar Anambara

Wani lamari mai cike da sarkakkiyar ban al’ajabi ya auku a garin Awo Idemili na jihar Anambara dake a shiyyar kudu maso gabashin kasar nan inda amarya ta haifi sambalelen saurayi kimanin awa biyu kafin a daura mata aure.

Ita dai amaryar mai suna Misis Chinezu Adeolisa ta bayyana wa duniya farin cikinta na samun sankacecen jariri a ranar ɗaurin aurenta da rabin ranta Mista Odeolisa.

NAIJ.com ta samu haka zalika cewa da yake tsokaci game da lamarin, angon Mista Odeolisa ya bayyana wannan al’amari da cewa daɗi kan daɗi ne.

Wato alhairai biyu, a lokaci guda.

Majiyar mu dai ta labarta mana yadda lamarin ya faru inda tace abin ya farune awoyi kaɗan kafin a fara shagalin ɗaurin auren, sai kawai nakuda ta kama amaryar. Nan da nan aka mika ta asibiti inda ta haife lafiya, ta samu ɗanta namiji.

Arewapro

My Name Is Ibrahim Ogah Oseyi, I am a Software Engineer and Seo expert. I want to help beginners who want to enter online industry to earn money through blogging & Freelancing I am a computer science engineer who takes blogging as a hobby. I like exploring things and sharing my experience with others.

Related Articles

Close
WhatsApp chat
%d bloggers like this:
Bitnami