Uncategorized

Na gode wa Allah Da yayi Ni Baki (Musa Mai Sana’a)Nagode wa Allah da ya yo ni baki‘ – jarumin kannywood ya mayar da martani game da sakon izgili da aka yi game da launin sa
Wata ma’abociyar dandalin sadarwa ta wallafa wani sako inda ta bada misali tsakanin launin fatan sa da abokin sana’ar shi Maishinku.

Shahararren jarumin barkwanci Musa mai sana’a ya mayar da martani game da wani sakon izgili da aka bada misali da launin fatan sa wanda ya mamaye kafafen sada zumunta.

A cikin wata sako da wata ma’abociyar twitter ta fitar ta rubuta “Yin bleaching ba shine matsalar ba sai kana tinanin zata haifa maka IBRAHIM MAISHINKU,  Kwatsam saiga MUSA MAI SANA’A”.

Sakon dai yayi yawo a shafuka da dama.

Da dama mutane sun mayar da batun abun dariya sai dai hakan na nuna godiya ga yadda Allah ya hallaci bawan sa.

Game da hakan jarumi ya fito fili yayi korafi game da sakon. A sakon da ya wallafa a shafin sa na Instagram jarumin barkwancin ya rubuta “AURAN FARAR MACE KO BATURIYA CE BA SHI ZAI SA A HAIFA MA FARIN DA BA HAIHUWAR FARI KO BAKI IKONE DAGA ALLAH, NI MAMANA FARACE TAS KUMA BAFULATANA CE HAR TA MANYANTA BABU KO DIGON BAKI A JIKINTA KUMA DUK WANDA YA TABA GANINTA YASAN MAGANATA HAKA TAKE, DON HAKA INA MATUKAR GODIYA GA ALLAH DAYAYONI BAKI KUMA ZUCIYATA FARA BAN DASHEBA MAANA NAI BLEACHING DON YANZU BAGA MATANBA BA GAMAZAN BA. BABBAN ABIN KUNYAMA NAMIJI DA BLEACHING KA TASHI KANEMI KUDI KA INGANTA RAYUWARKA DA SANAA YA FIYEMAKA IDAN KUMA BABU SANAARNE SAI A SAMAMUKU,ALLAH YA DATAR DA MU AMEEN”.

Arewapro

My Name Is Ibrahim Ogah Oseyi, I am a Software Engineer and Seo expert. I want to help beginners who want to enter online industry to earn money through blogging & Freelancing I am a computer science engineer who takes blogging as a hobby. I like exploring things and sharing my experience with others.

Related Articles

Close
WhatsApp chat
%d bloggers like this:
Bitnami