Uncategorized

Yadda Kwankwaso da Uche suka kore ni daga PDP – Malam ShekarauMalam Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar Kano, yace Uche Secondus, shugaban jam’iyyar PDP ta kasa da Rabiu Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano, sun taka rawar gani gurin fitar shi daga jam’iyyar adawa. Shekarau ya koma APC ne a ranar Asabar, washegarin da Adams Oshiomhole, shugaban APC da Abdullahi Ganduje, gwamnan jihar kano, suka same shi a gidan shi. Ya sanar da mabiyanshi cewa ya bar jam’iyyar adawa ne saboda shugabannin jam’iyyar sun ba Kwankwaso wuka da nama akan reshen jam’iyyar na jihar Kano bayan da ya dawo jam’iyyar a watan Yuli. A cikin watan yuli ne wasu daga cikin yan jam’iyyar APC suka koma PDP, har da Kwankwaso. Hakan yasa aka ba Kwankwaso wasu damammaki kamar haka:
Kashi 51 na cikin shugabancin jam’iyyar shi zai zaba. Sauran yan jam’iyyar su rike kashi 49. Sannan duk wani Dan takarar majalisar jiha ko ta tarayya da yazo ta gurin shi yana da tikitin zaben 2019. Rashin amicewa ta da hakan ne yasa na canza sheka, na gane cewa babu adalci. Inji Shekarau

Arewapro

My Name Is Ibrahim Ogah Oseyi, I am a Software Engineer and Seo expert. I want to help beginners who want to enter online industry to earn money through blogging & Freelancing I am a computer science engineer who takes blogging as a hobby. I like exploring things and sharing my experience with others.

Related Articles

Close
WhatsApp chat
%d bloggers like this:
Bitnami