Uncategorized

Sheikh Isa Alolo: Jarumi ya rasa yar uwar sa safiyar ranar sallah

Sheikh Isah Alolo

Shikh Isa Alolo ya rasa yayar sa Hajiya Binta Abubakar Isah safiyar ranar babban Sallah 21 ga watan Agusta.

Sanannen jarumi kuma mai shiryawa da bada umarnin fim a masana’antar Kannywood Isah Abubakar Alolo wanda aka fi sani da Sheikh Isa Alolo ya rasa yar uwar shi yayin bikin babban sallah.

Jarumin ya sanar da mutuwar yayar sa Binta Abubakar Isah a shafin sa na Instagram. Ta rasu safiyar ranar 21 ga watan agusta wanda tayi daidai da ranar babban sallah.

 

Ya rubuta “Innalillahi wa inna ilaihirraji’un. Allah yayi wa yaya ta rasuwa yau da safe, BINTA ABUBAKAR ISAH ALLAH ya gafarta miki BINTA Allah yasa mutuwa hutu ce A gareki, Allah yasa bakin wahalar ki kenan, Allah yasa Aljanna ce makomar ki…”

jim bayan sanar da lamarin sauran abokan sana’ar shi na Kannywood suke ta taya shi ta’aziya tare da jajanta masa inda suka wallafa hotunan marigayiyar a shafukan su na kafafen sada zumunta tare da yi mata addu’a.

Arewapro

My Name Is Ibrahim Ogah Oseyi, I am a Software Engineer and Seo expert. I want to help beginners who want to enter online industry to earn money through blogging & Freelancing I am a computer science engineer who takes blogging as a hobby. I like exploring things and sharing my experience with others.

Related Articles

Close
WhatsApp chat
%d bloggers like this:
Bitnami