Uncategorized

Bikin Sallah: Dalilin da yasa gwamnatin jihar Kaduna ta rufe wuraren shakatawa

A cikin wata sanarwa da aka fitar hukumomin jihar sun bayyana cewa fargabar tsaro shine babban dalilin daukar wannan matakin.

Ga masu bibiyan wuraren shakatawa da wasan yara a garin Kaduna yayin bikin sallah bana gwamnatin jihar ta bada umarni na a rufe su bisa ga wasu dalililai na matakin tsaro.

A cikin wata sanarwa da aka fitar hukumomin jihar sun bayyana cewa fargabar tsaro shine babban dalilin daukar wannan matakin.

A labarin da BBC ta fitar mai baiwa gwamnan jihar Kaduna shawar kan matakan tsaro Kanal Yusuf Yakubu ya shaida cewa tsoro fitina yasa suka dauki matakin rufe wuraren shakatawan.

Hadimin yace za’a yi hawan sallah kamar yadda aka saba yi a ko wani masarautu dake fadin jihar. Ya kuma kara da cewa gwamnan zai yi hawan sallah a garin Kafanchan bana.

Matakin dai zata hana ciniki ga masu wuraren shakatawan da dinbim yan kasuwa dake safara a farfajiyar. Wuraren shakatawa dake Kaduna su kan cika makil a lokutan bukuwan Sallah ko kirismeti.

Sai dai akwai wadanda ke jinjina ma gwamnatin bisa wannan matakin da ta dauka domin hakan zata hana kashe-kashe da fadace-fadace da ake yawan samu tsakanin matasa dake halartar wuraren.

Arewapro

My Name Is Ibrahim Ogah Oseyi, I am a Software Engineer and Seo expert. I want to help beginners who want to enter online industry to earn money through blogging & Freelancing I am a computer science engineer who takes blogging as a hobby. I like exploring things and sharing my experience with others.

Related Articles

Close
WhatsApp chat
%d bloggers like this:
Bitnami