Uncategorized

Bikin sallah: Yadda aka gudanar da sallar idi a Nijeriya(Hotuna)

Shugaba Buhari ya samu tarba bayan kammala sallah yayin da yake tattaki daga filin idi har zuwa layin gidansa dake nan Daura.

Nijeriya tare da sauran kasashen duniya da musulami dake fadin duniya suna murnar zagayowar bikin babban sallah.

Ga yadda aka gudanar da sallar idi a wasu jihohi dake Nijeriya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gudanar da sallar idi a nan mahaifar shi dake Daura nan jihar Katsina. Shugaban ya samu tarba bayan kammala sallar yayin da yake tattaki daga filin idi har zuwa layin gidansa.

 

Daruruwan masoya mazaunin garin daura suka yi masa gaisuwa. Shugaba ya halarci sallar idi ne tare da Sarkin Daura Alhaji Umar Faruk da sabon dan majalisar dattawa mai wakiltar yankin Daura Ahmed Babba-kaita.

Jihar Kano

Sarkin Kano mai martaba Muhammad Sanusi na biyu ya jagoranci sallar idi da aka gudanar a nan filin idi dake kofar Mata.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje tare da ma’aikatan gwamnatin jihar sun halarci sallar tare da yan majalisar masauratar kano.

Gwamna ya sha tarba daga masoyan shi a wurin sallar idin.

Jihar Kebbi

 

Babban Limamin Masarautar Gwandu Malam Ahmed Ibrahim Bashar ya Jagoranci sallah tare da Sarkin Gwandu Alh. Muhammed Iliyasu Bashar tare da Gwamnan Jihar Kebbi Sen Atiku Bagudu da Ministan Shari’a na Kasa Barr. Abubakar Malami SAN. da Manyan Jami’an Gwamnati da duban Daruruwan Musulmai.

Arewapro

My Name Is Ibrahim Ogah Oseyi, I am a Software Engineer and Seo expert. I want to help beginners who want to enter online industry to earn money through blogging & Freelancing I am a computer science engineer who takes blogging as a hobby. I like exploring things and sharing my experience with others.

Related Articles

Close
WhatsApp chat
%d bloggers like this:
Bitnami