Uncategorized

Dandalin Kannywood: Jarumin barkwanci Ayuba Dahiru ya rasu

Marigayi Ayuba Dahiru ya rasu safiyar ranar lahadi

Jarumin barkwanci ya rasu safiyar ranar lahadi bayan wata gajeruwar rashkn lafiya da yayi na kwana biyu.

Allah yayi wa Ayuba Dahiru jarumin barkwanci wanda ya fito a cikin shirin “Auren manga”  rasuwa.

Marigayin wanda aka fi sani da Tandu ya rasu safiyar ranar lahadi 19 ga watan Agusta bayan wata gajeruwar rashin lafiya da yayi.

Shahararren mai shirya fina-finai kuma wanda ya shirya shirin “Auren Manga” Falalu Dorayi ya sanar da labarin mutuwar sa a shafin sa na Instagram.

Ya Rubuta “Inna Lillahi wa inna ilayhi raji’un.Allah yaiwa Jarumin barkwanci AYUBA DAHIRU (TANDU) rasuwa.Ya rasu Yau Lahadi 19/8/2018.

Bayan gajeriyar rashin lafiya ta kwana biyu.

Allah ya jikansa yai masa rahma. Allah yasa mu cika da Imani.”

Jarumin wanda aka fi sani da tandu ya fito a fina-finan barkwanci hada da “Auren Manga” da “Gobarar titi. Ya rasu ya bar mata uku da yara tara.

Arewapro

My Name Is Ibrahim Ogah Oseyi, I am a Software Engineer and Seo expert. I want to help beginners who want to enter online industry to earn money through blogging & Freelancing I am a computer science engineer who takes blogging as a hobby. I like exploring things and sharing my experience with others.

Related Articles

Close
WhatsApp chat
%d bloggers like this:
Bitnami